Abinda Aka Raba a Walimar Yusuf Buhari da Zahra Bayero a Matsayin Tukwuici

 

Rabon Iphone 12 Pro aka yi a wajen walimar Yusuf Buhari da Zahara Bayero.

An ga sababbin wayar IPhone dauke da sunan Amarya da Ango da aka kyautar.

Rabon wadannan kaya masu tsada ya jawo mutane suna ta surutu a Facebook.

Abuja – Legit.ng Hausa ta samu labari cewa an raba kaya masu tsada a matsayin tukwuici ga wadanda suka samu halartar bikin ‘dan shugaban Najeriya.

Kamar yadda hotuna da bidiyoyi suka nuna an raba wani kwali da yake dauke da wayar Iphone da kuma na’urar Ipad, duk na kamfanin Apple, a wajen bikin.

An yi wa wannan kwali tambari da sunayen amarya da ango da ranar aurensu.

A ciki za a ga dambareriyar wayar Iphone 12 Pro wanda ake yayi a Duniya.

Haka zalika an sa man shafawa, littatafan rubutu da kuma kwalbar lemu a cikin kwalin kayan kyautan. Bugu da kari a wani kwali na dabam, akwai sabuwar na’urar Ipad ta zamani.

A jikin Ipad din da wayar ta IPhone 12 Pro, akwai sunayen amarya da angonta.

Ganin wadannan kaya na musamman da aka ba mahalarta, mutane sun fito suna ta tofa albarkacin bakinsu, musamman a irinsu dandalin Facebook.

Me mutane ke fada?

Injiniya Aminu Bello yace da wannan dawainiyar miliyoyi da aka yi, za a iya sayen tireloli a raba wa ‘yan gudun hijiran da jahohin Katsina da Zamfara kayan abinci. Muhammad T. Shehu kuwa cewa ya yi dangin amarya watau Mai martaba, Nasiru Ado Bayero ne suka dauki nauyin raba wadannan kaya masu ‘dan Karen tsada.

Rabi’u Biyora ya buge ne da da-na-sani, yace da ya san za a samu IPhone 12 Pro da IPad, da ya halarci walimar ko da zai biya kudin jirgi, domin zai tashi da riba.

Kamfanin apple ya bada na shi gudunmuwan Shine Baba yace a raba ma talakawa saboda son da yake masu.

– Aliyu Tafashiya

Duk kanwan jace! Talaka yakamata kwatakwata yadaina tunanin akwai mai sonshi a Nigeria.

– Isa Maina

Kabiru Danladi

wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa, ya tuna da yadda aka raba manyan wayoyin IPhone a lokacin da Goodluck Jonathan ya aurar da ‘ya ‘yansa a 2014.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here