Kotu ta Dakatar da Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Uche Secondus

 

Rivers – Rikicin babbar jam’iyyar hamayya PDP ya sake ɗaukar eani sabon salo ranar Litinin a jahar Ribas, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Wata babbar kotu a jahar Ribas ta dakatar da Uche Secondus daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP na kasa.

Secondus, wanda yake ta faɗi tashin tike mukaminsa, an ba shi damar ya shirya gangamin taron jam’iyyar a watan Oktoba.

Legit.ng Hausa ta gano cewa Secondus ya matsa cewa dole a bar shi ya karasa wa’adin mulkinsa.

Kotu ta dakatar da Secondus daga ɗaukar kansa Shugaba

Mai shari’a O. Gbasam, ya tumɓuke Uche Secondus daga matsayin shugaban PDP yayin da yake yanke hukunci kan karar jiga-jigan PDP suka shigar akansa.

Waɗanda suka shigar da karar sun haɗa da, Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da kuma Umezirike Onucha.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here