Gidauniyar Qatar da Tallafawar Gidauniyar Malam Inuwa ta Rabawa Marayu Kayan Sallah a Jihar Jigawa

 

Gidauniyar ayyukan jinƙai da taimakon al’umma ta ƙasar Qatar ta gudanar da rabon tallafin kayan sallah ɗinkakku ga yara marayu mata da maza sama da mutum (100) a Jihar Jigawa bisa tallafawar gidauniyar ba da agaji, taimako, jinƙai da ayyukan alkhairi ta Malam Inuwa, wacce mai girma shugaban hukumar (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) ya kafa.

Taron rabon kayan wanda aka gudanar a ɗakin taro na makarantar koyon aikin jinya da ungurzoma da ke Haɗejia a wannan rana, ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin jagoran tawagar gidauniyar ta ƙasar Qatar, Shaik Hamdi da shugabannin gidauniyar Malam Inuwa, ƙarƙashin jagorancin Dakta Hussaini Baban.

Da ya ke jawabi, jagoran tawagar gidauniyar ta Ƙasar Qatar, Shaik Hamdi ya yabawa gidauniyar Malam Inuwa da fadar mai martaba sarkin Haɗejia a bisa haɗin kai da ƙarfafa gwiwar da su ke ba su a duk lokacin da su ka nufaci gudanar da ire-iren waɗannan ayyukan alheri.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban gidauniyar ta Malam Inuwa, Dakta Usaini Yusuf Baban ya bayyana godiya da addu’ar fatan alkhairi ga gidauniyar bisa wannan ayyuka da su ke yi, inda ya jadda aniyarsu ta cigaba da marawa ayyukan gidauniyar baya duba da yadda ita ma gidauniyar ta Malam Inuwa ta ke ƙoƙari kan wannan aiki inda ko da a wannan wata na Ramadan ta yi rabon tallafin shinkafa ga marayu ɗari-ɗari a kowacce ƙaramar hukuma tare da raba kayan sallah ga marayu da dama.

Haka zalika kuma, taron ya samu halartar sakataren kwamitin marayu na Jihar Jigawa Shaik Abdulƙadir Zakar, da na’ibin limamin masarautar Haɗejia, Malam Umar Hamza Abbas haɗi da sauran masu ruwa da tsaki.

Yara marayun da su ka amfana da wannan tallafi sun bayyana farin cikinsu matuƙa da godiya bisa wannan abin alkhairi da aka yi musu gami da addu’ar Allah Ya ba da lada.

Juma’a, 29 ga watan Afrelu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here