‘Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Tsagin APC a Jahar Bayelsa Sunday Frank-Oputu

Bayelsa- Wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe wani shugaban tsagin APC a jihar Bayelsa Sunday Frank-Oputu.

The Nation ta tattaro cewa an kashe Frank-Oputu, dan kabilar Igbomotoru ne a karamar hukumar Ijaw ta Kudu, a daren ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, a gidansa dake Yenezue-gene a Yenagoa.

Jaridar ta ruwaito cewa, ana zargin cewa maharan sun harbe shi ne ta tagar gidansa da ke bude don samun iskar Allah saboda babu wutar lantarki a unguwarsu.

Frank-Oputu na daya daga cikin wadanda suka fafata wajen gano ingancin taron taron gangamin APC na mazabu a Bayelsa.

A wancan lokacin ya kuma yi Allah-wadai tare da bibiyar harin da aka kai wata babbar kotu inda aka jefi alkalin kotun, Mai shari’a Nayai Aganaba da kwalabe.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here