Cire Tallafi: An Rage Shigo da Fetur da Lita Biliyan 2.58 – Gwamnatin Tarayya

 

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta ce Najeriya ta samu ragowar shigo da man fetur bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a watan Mayun 2023.

Hukumar ta ce an samu ragowar shigo da fetur ɗin daga lita biliyan 20.30 a 2023 daga lita biliyan 23.54 da aka shigo da shi a shekarar 2022, wanda hakan ke nufin ragowar kashi 13.77 cikin 100.

“Maganar shigo da man fetur, an shigo ga lita biliyan 20.30 a shekarar 2023, maimakon lita biliyan 23.54 na shekarar 2022, wato an samu ragowa da kashi 13.77. Ragowar ma za ta fi bayyana ne idan aka kwatanta da wata shidan ƙarshe na shekarar 2022.

“A wata shidan karshe na 2022, man da aka shigo da shi ya kai lita biliyan 11.98, wanda ke nufin ragowar kashi 30.22 idan aka kwatanta da wata shidan farko na 2023, wato ragowar lita biliyan 3.62.

Shi ma ministan yaɗa labarai na ƙasar Idris Mohammed ya ce amfani da man fetur ya ragu da kashi 50 a ƙasar bayan cire tallafin man fetur da aka yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Logged in as Khadija Garba. Log out?

Please enter your comment!