Rahoto ya Bayyana Yadda Afirka ta Kudi ta Gawurta Wajen Aikata Laifuka
Alƙaluman aikata laifuka na baya-bayan nan da aka fitar na Afirka ta Kudu “abu ne mai muni kamar na baya”, a cewar Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Bheki Cele.
Kamar yadda shafin Twitter na gwamnati ya bayyana, ministan ya ce bayanan na watan Yuli zuwa Satumba sun nuna cewa Afirka ta Kudu “gawurtacciyar ƙasa ce wajen aikata laifuka”.
Read Also:
A cewarsa, aikata kisan kai ya ƙaru da kashi 21 cikin 100 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin na shekarar da ta gabata.
Game da cin zarafi ta hanyar lalata kuwa, ya ce an yi wa mutum 9,500 fyaɗe cikin wata uku – abin da ke nufin duk awa ɗaya ana aikata fyaɗe sau huɗu. Lamarin ya ƙaru da kashi 7 kenan cikin 100.
“Wajibi ne a ƙara ƙoƙari wajen tabbatar da cewa an kare rayukan ‘yan Afirka ta Kudu,” in ji Mista Cele.