An Buɗe Rijistar Karrama Zaƙaƙuran Matasan Arewa 30 Ƴan Ƙasa da Shekaru 30 Karo na Farko – Taskar Nasaba

Kafar yaɗa labarai ta Arewa Agenda haɗin guiwar Taskar Nasaba Jaridar PRNigeria da Daily Nigerian sun samar da wani dandamali na karrama matasa 30 ƴan ƙasa da shekaru 30 mai laƙabin (Arewa Star Awards ASA2022).

Wannan na ƙunshe a Sanarwa da Shugaban Jaridar Arewa Agenda Muhammad Ɗahiru Lawal ya fitar, inda yace babban taron bada lambar yabon za’a gudanar da shi ne cikin watan Disamba a jihar kano, taron da zai tattara fitattun mutane da Ƙwararru a fannoni daban daban na Arewa da Najeriya kwata. An samar da wannan bikin domin zaƙulu wasu fitattun matasa haziƙai dake yankin Arewacin Nijeriya guda 30 waɗanda kuma ke da shekaru ƙasa da 30 da haihuwa dake gudanar da ayyuka masu inganci da tasiri a sassa daban-daban da suka jibanci rayuwar Ɗan Adam.

Kyautar Arewa Stars Award “data haɗa haziƙan matasa” zata karrama matasa 30 waɗanda basu wuce shekaru 30 ba, inda zasu karbi kyaututtuka 30 a fannoni 30 da suka haɗa da Sadarwa, Ilimi, Siyasa, kafar sadarwa ta zamani, Ado da kwalli, Nishaɗi, fintech, shari’a gami da ƙirƙira.

Sauran ɓangarorin sun haɗa da sana’oin dogaro da kai, Magunguna (kiwon lafiyar Al’umma) aikin Banki, Adon gidaje, Jogoranci, wasanni, Zanen Gini da ƙere-ƙere, Jaruman wasannin kwakwaiyo Maza da Mata, masu zane-zane damasu, zanen Abu mai Mutsi, zaƙaƙurai a fannin tallafawa Ɗan Adam, Sana’oin Hannu (takalma, Jaka, Rini, ɗinki) rajin kare haƙƙi /aiki da harkokin sanarwa da fasaha da hada hadar gidaje.

Babban taron karramawar zai ƙunshi Muhimman abubuwa kamar bayar da kyaututtuka ga Matasa 30 dake ƙasa da shekaru 30, ƙwarya-ƙwarya tattaunawa, bajakolin Fasaha, kyautar girmamawa ga jagorori da masu ayyukan tallafawa Al’umma, girmama wasu ƙungiyoyi, Nishaɗi, (Mawaƙa da Jaruman wasan kwaikwayo) liyafar cin abincin Dare da kuma ƙaddamar da littafin Labaran karyar 101 kan zanga-zangar EndSARS da aka fassara zuwa harshen Hausa.

Masu shiga za su iya zaɓar ƙungiyoyi, ɗaiɗaikun mutane da masu ba da Agaji dake tallafawa matasa don samun lambobin na girmamawa. Waɗanda suka lashe babbar kyauta daga ko wanne nau’i za su zama jakadunmu don ci gaba mai dorewa kuma za’a yi musu laƙabi da “TAURARON AREWA .”

Za’a rufe shiga wannan gasa a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2022 za’a fara zaɓen waɗanda suka yi nasara mako guda bayan fidda sunayen waɗanda suka yi nasara daga kwamitin alkalan gasar. Kwammitin Tantancewar ya ƙunshi masana daga kowani fanni na rayuwa domin tabbatar da adalci ga kowa. Zaku iya bada tallafi ko ɗaukar nauyi ko bada tallafi a taron.

Domin samun damar shiga wannan gasar ta karrama matasa 30 Ƴan ƙasa da Shekaru 30 a ko wanne fanni sai a bi: https://bit.ly/3rKdxiF.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here