An Hallaka Mutum Biyu a Harin Coci a Jihar Kogi

 

Wasu ɓata gari sun kai hari cocin Celestial da ke Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, inda suka kashe mutum biyu tare kuma da jikkata wasu da dama.

Shaidu sun bayyana Jaridar Daily Trust a Najeriya cewa ɓata garin sun yi dirar mikiya a cocin ne da misalin 8:00 na yammacin ranar Lahadi, inda suka bude wuta kan mambobin cocin da suka je yin addu’a.

An ruwaito kwashe gawakin mutanen biyu da suka mutu daga cocin zuwa Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Lokoja, yayin da su kuma wadanda suka jikkata aka garzaya da su zuwa wani asibiti domin yi musu magani.

Kakakin ‘yan sandan Jihar, SP Williams Ayah, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta aike da jami’anta zuwa yankin domin kamo wadanda suka kai harin.

Harin dai shine irin sa na biyu da aka kai wa wata coci a baya-bayan nan a Jihar ta Kogi, inda a makonni da suka gabata ma aka kai hari kan wata majami’a a Sarkin Numan na yankin Felele na jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here