Rami ya Rufta da Mahaka Ma’adanai a Jahar Benue, 3 Sun Rasa Rayukansu

 

A jahar Benue, wasu mahaka ma’adanai sun hallaka yayin da suke tsaka da aiki a cikin rami.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Talata 28 ga watan Satumba.

Shugaban karamar hukumar yankin da lamarin ya faru ya bayyana gaskiyar yadda lamarin ya faru.

Benue – Mutane uku sun mutu bayan da wata mahakar ma’adanai da suke aiki a ciki ta rufta a yankin Anyiin da ke karamar hukumar Logo a jahar Benue, ranar Talata 28 ga watan Satumba.

Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa marigayan sun kasance suna cikin hako ne lokacin da ramin ya rufta dasu.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce mamatan sun mutu nan take yayin da mutanen gari kuwa suka yi kokarin ceto wadanda suka jikkata.

Shaidu sun ce wasu kalilan da suka jikkata an kai su asibiti nan da nan don duba lafiyarsu.

Da aka tuntube shi, shugaban karamar hukumar Logo, Kwamared Terseer Agber, ya ce duk da bai san da masu hakar ma’adinan a yankinsa ba, kamfanin, duk da haka, ya shigo da takardunsa (wai daga gwamnatin tarayya) kuma sarakunan yankin sun ba shi izinin aiki.

Agber ya ce:

“Da sanyin safiyar yau (Talata), aka kira ni aka sanar da ni cewa kimanin mutane hudu sun makale a ramin hakar ma’adinai. Don haka na ba da umarni cewa a yi kokari a yi wani abu kuma daga baya sun dawo sun ba da rahoton cewa sun gano gawarwaki uku da guda daya da ya jikkata.

“Na sha kiran a yi taro tare da su don warware lamarin, amma duk da haka taro ya gagara. Gwamnatin jahar na sane da ayyukan su a yankin.

“Gwamna Samuel Ortom ya tura Kwamishinoni guda biyu ciki har da na Noma; Filaye, Bincike da Ma’adanai masu karfi, amma babu abin da ya faru.

“Masu hakar ma’adinan sun ce ba su da wata alaka da gwamnatin jahar, cewa sun samo lasisin su ne daga Abuja kuma dama hakki ne na Gwamnatin Tarayya, ba su da wata alaka da gwamnatin jahar Benue.”

A halin da ake ciki, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Benue, DSP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu wani bayani game da lamarin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here