Yadda na Kusa Rasa Kujerata a Karo na Biyu – Gwamna El-Rufa’i
Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana yadda ya kusa rasa kujerarsa a karo na biyu saboda shirin yi wa malaman jahar gwaji.
Gwamnan na jahar Kaduna ya ce ya so sadaukar da komai nasa don ganin yara sun samu ingantaccen ilimi a jaharsa.
El-Rufai ya bayyana cewa ya fuskanci barazana game da shan kaye a zabe amma ya ce lallai sai an yi wa malaman gwaji don kawai ya cimma manufarsa.
Kaduna – Gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi bayanin yadda ya so sadaukar da kudirinsa na zarcewa a karo na biyu don bai wa yaran jaharsa ilimi mai inganci.
Da yake magana a wani taro da aka gudanar a Ado-Ekiti, jahar Ekiti, El-Rufai ya ce an yi masa barazana da shan kaye a zabe, Channels TV ta rawaito.
El-Rufai ya ce ya dage sannan ya aiwatar da gwajin kan malamai a Kaduna duk da barazanar.
“An ce dan uwana a nan ya fadi takararsa na biyu a karon farko saboda yayi barazanar yiwa malamai gwaji.
“Na gwada su sannan na sallame su kafin zabenmu. Da aka ce mun zan rasa kujerana a karo na biyu, nace idan rasa kujeran zai ba yaran jahar Kaduna makoma mai kyau da ilimin firamare mai inganci, toh na shirya hakura da shi.”