Dakarun  Najeriya Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji fiye da 40
‘Yan fashin daji fiye da 40 ne sojojin Najeriya suka kashe a yankin arewa maso yamma cikin mako biyu, a cewar rundunar.
Muƙaddashin shugaban sashen yaɗa labarai na rundunar, Benard Onyeuko, shi ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis yana mai cewa lamarin ya faru ne a jahohin Sokoto da Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Da yake magana a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja, babban jami’in sojan ya ce an gudanar da hare-haren daga 1 zuwa 13 na watan Oktoba.
Kazalika dakaru sun lalata sansanonin ‘yan bindigar da dama, a cewarsa.
A farkon watan Oktoba ne Babban Hafsan Sojan Ƙasa Janar Faruk Yahaya ya ƙaddamar da wasu sabbin ayyukan soja uku da zummar daƙile matsalar tsaro a Najeriya.
Ayyukan da suka haɗa da Golden Dawn da Still Water da Enduring Peace, dakarun Najeriya za su gudanar da su ne a sassa daban-daban na ƙasar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here