Kamfanin Gazprom na Kasar Rasha ya Kulle Bututun Iskar Gas Zuwa Kasar Poland da Bulgaria

 

Kamfanin da ke samar da makamashi na Rasha Gazprom ya sanar cewa ya kulle bututun da ke jigilar iskar gas zuwa kasar Poland da Bulgaria bayan da kasashe biyun suka ki biyan kudin kayan da kudin Rasha wato rouble.

Tun farko kasashen biyu wato Poland da Bulgariya sun ce Rasha ta sanar da su a hukumance cewa za ta kulle bututun.

Sanarwar kamfanin na Gazprom ya biyo bayan bayanan da ke cewa iskar gas din ta ci gaba da shiga kasar Poland da sanyin safiyar yau Laraba amma daga baya Poland ta sanar cewa gas din ya daina isa kasarta.

Cikin wata sanarwa, kamfanin makamashi na Poland ya yi tir da matakin na Rasha, yana cewa “matakin ya karya yarjejeniyar da Rasha da Poland suka kulla”.

Bulgariya ma ta tuhumi Rasha da karya yarjejeniyar kasuwanci iskar gas tsakaninsu.

Sai dai zuwa wannan lokacin da muke hada wannan rahoton, sauran kasashen Turai na ci gaba da samu iskar gas daga Rasha.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here