Jam’iyyar APC ta Nemi Ministocin Buhari da ke Son Takara a 2023 da su Ajiye Aiki

 

Domin kaucewa taka dokar zabe ta Najeriya, jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta bayyana ranar karshe da ministoci da masu rike da mukaman gwamnati ya kamata su ajiye ayyukansu a matakan tarayya da na jihohi idan suna son tsayawa takara a zabukan da ke tafe.

Jami’an gwamnatin na da zuwa ranar Asabar 30 ga watan Afrilu su ajiye mukaman nasu.

Matakin ya shafi wasu ministocin gwanatin Buhari kamar ministan sufuri Chibuike Rotimi Amaechi da kwadago Chris Ngige, suna ciki jami’an da suka bayana aniyarsu ta tsayawa takara.

Sashe na 3(i) na dokar jam’iyyar APC kan tsayar da ‘yan takara a zaben 2023 na cewa: “Ba a yarda wani jami’in da ke rke da mukami a kowane matakin gwamnati ya zama deleget ko a zabe shi domin fitar da ‘yan takara.”

Jadawalin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar ya tsara cewa jam’iyyun siyasa na da zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin su mika ma hukumar mutanen da suka tsayar a zabukan da ke tafe.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here