Rasha ta yi Martani Kan Rashin Gayyatarta Jana’izar Sarauniya Elizabeth
Jami’an ma’aikatar diflomasiyyan kasar Rasha sun ce rashin gayyatarsu jana’izar Sarauniya Elizabeth bai dace ba.
Gwamnatin ta Rasha tace ofishin jakadancin Birtaniya ta aike mata da sakon daliln rashin gayyatarsu.
Masarauta da gwamnatin kasar Ingila ta sanar da cewa za’a yi jana’izar Sarauniyar Elizabeth II ranar Litinin 19 ga watan Satumba, 2022.
Read Also:
Gwamnatin kasar Rasha ta caccaki gwamnatin Birtaniya kan rashin gayyatar jami’anta jana’izar Sarauniya Elizabeth II, tace wannan rashin kyautatawa ne.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha, Maria Zakharova, a ranar Juma’a ya ce gwamnatin Birtaniya tace da an ki gayyatar Rasha ne saboda yakin da wakana a kasar Ukraine.
A jawabin Maria Zakharova, ya tuhumci Birtaniya da nuna son kai da goyawa Ukraine baya, rahoton NAN.
A cewarsa:
“A ra’ayinmu ana son amfani da matsalar da ta shafi kowa wajen cimma wata mafita ta fito-na-fito da kasarmu kuma wannan rashin hallaci ne.”
“Elizabeth II babbar mutum ce kuma bata yi katsalandan cikin harkokin siyasa ba, amma hakan bai hana gwamnatin Birtaniya sakin jawabin raba kan mutane ba.”