Kuma Dai, Kotu ta Dage Zaman Gwamnatin Tarayya da ASUU

 

Kotun Ma’aikata Ta Kasa ta dage zaman karar da gwamnatin tarayya ta shigar kan kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) zuwa ranar Litinin 19 ga Satumba, 2022.

A zaman da akayi ranar Juma’a, lauyan Gwamnati, James Igwe, ya bukaci kotu ta gaggauta yanke hukunci kan wannan lamari saboda muhimmancinsa don dalibai su koma makaranta.

Igwe ya bayyana kotu cewa tunda yanzu ana shari’a, ya kamata Malamai su janye daga yajin aiki zuwa ranar yanke hukunci, rahoton ChannelsTV.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here