Rashin Fitowar Mutane Zaɓe a Yau, Rashin Cikakken Shiri ne Daga INEC – Atiku Abubakar
Dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar PDP a zaɓen da ya gabata Atiku Abubakar ya ɗora alhakin ƙarancin fitowar jama’a rumfunan zaɓen gwamna kan hukumar zaɓen ƙasar, da ake gudanarwa yau a faɗin ƙasar.
Atiku Abubkar wanda ya kaɗa ƙuri’arsa a birnin Yola da ke jihar Adama ya koka kan rashin fitowar jama’a rumfunan zaɓen, wanda ya ɗora alhakin hakan kan hukumar INEC ne.
“Abin takaici ne, rashin fitowar mutane zaɓe a yau, rashin cikakken shiri ne daga INEC ya sa ta gabatar da sakamako marar inganci a zaɓen ranar 25 ga watanb fabrairu”.
Read Also:
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar wanda ya zanta da manema labarai bayana kaɗa ƙuri’arsa ya ce yana fatan hukumar zaɓen ƙasar za ta yi amfani da wannnan dama domin gyara kura-kuran da suka yi a baya.
Sai dai har yanzu INEC ɗin ba ta mayar da martani kan zargin ba.
“Ban iya ma fito da waya ta ba lokacin da yaran nan suka zo, suka ringa dukan motata, suka fasa min madubin gefe na mota…” tana magana ne a lokacin da take barin rumfar zaɓen.
Bayelsa: Rahotanni na cewa wasu ƴan daba sun kwace tare da lalata kayan zaɓen ɗan majalisar dokoki a rumfuna masu lamba 02 da 03 da 04 da kuma rumfa ta 05 a mazaɓa ta biyar a ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa, kamar yadda kafofin yaɗa labarai na jihar suka rawaita.
A nasa ɓangaren, gwamna Douye Diri ya yi Allah wadai da da harin da kakkausar murya, yana mai kira ga babban sufeton ƴan sanda na ƙasa da kwamishinan ƴan sandan jihar Bayelsa su maido da zaman lafiya a yankin, kamar yadda mai taimaka masa a harkokin kafofin watsa labarai Daniel Alabrah ya tabbatar a shafinsa na Faceook.