Abinda ya Kara Karfin Rashin Tsaro Musamman a Arewa Maso Gabas – Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu Sani ya alakanta talauci ta karyewar tattalin arziki da ta’addanci a arewacin Nigeria.
Shehu Sani ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke martani kan hare-haren da ake kai wa Arewa maso Gabashin Nigeria.
Sanata Sani ya bayyana damuwarsa kan rahoton cewa yan ta’adda na raba wa mutane N20,000 a gidajensu a jahohin Borno da Yobe.
Tsohon sanatan Kaduna mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya ce talauci da wahalhalun da talakawa ke ciki ne ke karar rura wutar rashin tsaro musamman a Arewa maso Gabas.
Read Also:
Shehu Sani ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke martani kan hare-haren da yan ta’adda ke kaiwa a Arewa maso Gabas da wasu sassan kasar.
Da ya ke kokawa kan matsalolin a Twitter a ranar Talata, tsohon dan majalisar ya bayyana damuwarsa game da sabon tsarin da yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ke yi na raba wa mutanen da suke kaiwa hari kudade a Yobe da Adamawa.
“A watan da ta gabata, Yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun rabawa mutanen garin da suka kai wa hari N20,000; Yanzu kuma yan ta’addan ISWAP na rabon kayan abinci a wasu garuruwa a jahohin Yobe da Borno; Darasin a nan shine akwai mummunan talauci da ke rura wutar ta’addanci a Arewa maso Gabashin kasar mu.
“Idan yan ta’adda sun kashe talakawa, yan ta’addan miyagu ne; Idan yan ta’adda sun ciyar da talakawa, gwamnati ce muguwa,” kamar yadda Shehu Sani ya kara rubutawa a Twitter.