Champions League na 14: Real Madrid ta Doke Liverpool

Real Madrid ta dauki Champions League na bana, bayan doke Liverpool 1-0 a karawar da suka yi a filin Stade de France da ke birnin Paris din Faransa ranar Asabar.

Vinicius Junior ne ya ci kwallon da ya bai wa Real Madrid damar lashe Champions League na 14 jumulla kenan.

Vinícius Júnior ya ci kwallo hudu kenan ya kuma bayar da shida aka zura a babbar gasar Zakarun Turai ta bana.

Wannan bajintar ta sa ya zama na farko daga Kudancin Amurka da yake da hannu a cin kwallo 10 a matakinsa mai shekara 21 da haihuwa a kaka daya a UEFA Champions League.

Wanda keda wannan tarihin shi ne Lionel Messi, mai shekara 21 a kakar 2008-09, wanda keda hannun a cin kwallo 14, ya zura tara ya kuma bayar da biyar aka jefa a raga.

Wannan si ne wasa na tara da suka fuskanci juna a Champions League, inda Real Madrid ta yi nasara a biyar, Liverpool ta ci uku da canjaras daya.

Real Madrid ta dauki kofi na 13 a kan Liverpool, bayan da ta doke ta 3-1 ranar 26 Mayun kakar 2017/18.

Real Madrid ita ce ta lashe La Liga na kakar nan, kuma na 35 jumulla, ta kuma dauki Champions League 14 jumulla – 1955-56, 1956-57, 1957-58, 1958-59, 1959-60, 1965-66, 1997-98, 1999-2000, 2001-02, 2013-14, 2015-16, 2016-17, 2017-18 da kuma 2021/22..

Ita kuwa Liverpool tana da babban kofin gasar Zakarun Turai guda shida – 1976-77, 1977-78, 1980-81, 1983-84, 2004-05, 2018-19.

Tun farko Liverpool ta sa ran daukar kofi hudu a kakar nan, ta kuma lashe Carabao Cup da FA Cup a bana, amma Premier League ya gagare ta, bayan da Manchester City ta dauki na shida jumulla ranar Lahadi.

City ta yi nasarar lashe Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool, wadda ta kasa daukar Champions League na 2021/22 a hannun Real Madrid ranar Asabar.

Ga tarihin jerin haduwa tara tsakanin kungiyoyin:

Kakakr 2021/22

Champions League wasan karshe Asabar 28 ga watan Mayu

Liverpool 0 – 1 Real Madrid
Kakar 2020/2021

Champions League Laraba 14 ga watan Afirilu

Liverpool0 – 0Real Madrid
Champions League Talata 6 ga watan Afirilu

Real Madrid3 – 1Liverpool
Kakar 2017/2018

Champions League wasan karshe Asabar 26 ga watan Mayu

Real Madrid3 – 1Liverpool
Kakar 2014/2015

Champions League Talata 4 ga watan Nuwamba

Real Madrid1 – 0Liverpool
Champions League Laraba 22 ga watan Oktoba

Liverpool0 – 3Real Madrid
Kakar 2008/2009

Champions League Talata 10 ga watan Mayu

Liverpool4 – 0Real Madrid
Champions League Laraba 25 ga watan Fabrairu

Real Madrid0 – 1Liverpool
Kakar 1980/1981

European Cup Laraba 27 ga watan Mayu

Liverpool1 – 0Real Madrid
Wadanda suka buga wa Real Madrid wasan:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Fuidias.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo, F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco, Camavinga.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Jović, Bale, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here