Real Madrid ta Nemi PSG da ta Saida Mata Kylian Mbappe Akan $188

 

Kylian Mbappe ya ki sabunta kwantiraginsa da Paris Saint-Germain.

Real Madrid tana neman a saida mata ‘dan wasan a kan miliyan $188.

Idan ciniki ya fada, ‘Dan wasan gaban zai bar Lionel Messi da Neymar.

Mbappe yana neman barin PSG ne?

Paris – A karshen kakar shekarar banan ne wa’adin ‘dan wasan gaban kasar Faransa, Kylian Mbappe zai kare a kungiyar Paris Saint-Germain.

Rahotanni daga Goal.com sun bayyana cewa sau shida Paris Saint-Germain tana neman ‘dan wasan ya sabunta kwantiraginsa, amma ya ki yarda.

Tuni Real Madrid ta bukaci PSG ta saida mata ‘dan wasan, ta kuma gabatar da fam miliyan €160 (£137m/$188m) domin a sallama mata tauraron.

A lissafin kudin mu na gida, wannan zunzurutun kudi ya tashi a kan kusan Naira biliyan 80 kenan.

Da gaske Real Madrid ta ke yi

Rahoton ya nuna kungiyar ta Madrid tana sa ran ta iya dauke Kylian Mbappe mai shekara 21 kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasan shekarar nan.

Duk da cewa Real Madrid tana fama da karancin kudin-shiga a dalilin annobar COVID-19, ta dage a kan dauko daya daga cikin taurarin da ake ji da su.

A ina aka tsaya a cinikin?

Shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Perez da kansa ya shiga cikin wannan ciniki. Yanzu haka kungiyoyin na cigaba da tattunawarsu a asirce.

Akwai kyakkyawar alaka tsakanin Florentino Perez da shugaban kungiyar PSG, Nasir El-Khelafi, sannan Mbappe yana sha’awar buga wa Real Madrid.

Yanzu inda matsalar ta ke shi ne kungiyoyin biyu su amince da farashin da za a saida ‘dan wasan domin ba zai yi wahalar amince wa da koma wa Sifen ba.

Da aka tambayi Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti a game da ‘dan wasan, yace bai san ko za a kawo masa shi ba, amma yace yana da ‘yan kwallonsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here