Shugaban Jam’iyyar PDP na Jahar Lagos, Adegbola Dominic ya Mutu

 

Shugaban babbar jam’iyyar adawa PDP, reshen jahar Lagos, Adegbola Dominic, ya kwanta dama.

Kakakin jam’iyyar na jahar, Taofeeq Gani, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Yace za’a sakko da tutocin PDP dake faɗin jahar Lagos zuwa rabi domin nuna alhinin mutuwarsa.

Lagos – Shugaban jam’iyyar PDP reshen jahar Lagos, Adegbola Dominic, ya kwanta dama, kamar yadda Punch ta rawaito.

Kakakin PDP na jahar, Taofeeq Gani, shine ya tabbatar da mutuwar ga wakilin Punch ta wayar salula.

Gani ya bayyana cewa shugaban PDP na jahar Lagos ya mutu ranar Laraba da yamma bayan fama da cutar da ta shafi COVID19.

Cutar Korona ta yi ajalin shugaban PDP

A wani jawabi da ya fitar, Gani yace:

“Shugaban PDP na jahar Lagos ya mutu bayan fama da cutar COVID19, Marigayin wanda babban ma’aikacin lafiya ne, ya kasance ɗan siyasa na daban wanda ya amince da zuba mafi yawan kuɗinsa a hanyar da mutane zasu ji daɗi.”

“Kafin mutuwarsa Dakta Dominic, shine shugaban asibitin Santa Maria.Ya rike mukamai da dama a tarihin siyasarsa.”

“Marigayin ya rike ofishin SDF na jaha, shugaban PAC na jaha, Shugaban jam’iyyar PAN ta ƙasa, da shugaban jam’iyyar PDP ta jahar Lagos.”

Wace kujerar mulki ya rike?

Gani ya kara da cewa ya taba tsayawa takarar gwamnan jahar Lagos karkashin inuwar jam’iyyar APGA.

Hakanan shine ɗan takarar kungiyar Jakande a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar SDP a kujerar sanatan Lagos ta yamma, inda ya fafata da Bola Tinubu.

Bugu da kari, Gani yace a koda yaushe burin marigayi Dominic shine cigaban jahar Lagos kuma tabbas zai yi dana sanin barin jahar ba yadda yaso ba.

Za’a sauke tutocin PDP a Lagos zuwa rabi

Mista Gani yace za’a jima ba’a manta da marigayi Adegbola Dominic a siyasar jahar Lagos ba, kamar yadda the nation ta rawaito.

“Muna mika ta’aziyyar mu ga iyalansa. Za’a sauke dukkanin tutocin PDP zuwa rabi kuma duk wani taron PDP a wannan lokacin zai kasance addu’a ce gare shi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here