An Samu Kungiya a Kasar Afghanistan Masu Adawa da Mulkin Taliban

 

A can kasar Afghanistan, an samu wasu sojojin da suke adawa da mulkin kungiyar Taliban.

Rahoto ya bayyana cewa, sun harba wani babban makami cikin kwari domin nuna adawarsu ga Taliban.

Sun kuma bayyana manufarsu na kifar da gwamnatin kungiyar Taliban matukar ta yi yunkurin kai musu farmaki.

Afghanistan – A saman wani tsauni mai mamayewar bakin haure tsawon shekaru da dama, wasu mayakan dake adawa da mulkin Taliban sun harba babban makami a cikin wani kwari mai zurfi a Panjshir, AlJazeera ta rawaito.

Mayakan sun kasance mambobi ne na National Resistance Front (NRF) – babbar fitacciyar kungiyar adawa ta Afganistan da ta fito tun lokacin da Taliban ta kame Kabul kwanaki tara da suka gabata.

Tare da mayakan kungiyar da tsoffin sojojin gwamnati masu mukamai, NRF ta kafa buhunan bindigogi, harsasai da wuraren sa ido wadanda aka yi da buhunna cike da kasa don kare farmakin Taliban a sansaninsu da ke a Kwarin Panjshir.

Mayakan, da yawa suke sanye da kakin sojoji, suna sintiri a yankin a cikin manyan motocin Humvees masu dauke da bindigogi a baya da aka ce kirar Amurka ne.

Wani mayaki a tsaunin na Panjshir, da yake lissafa nasarorin da suka samu a baya kan ‘yan Taliban ya ce:

“Za mu goga fuskokinsu a cikin kasa.”

Su waye a asalin yankin Panjshir?

A tsaunin dake da cikakken tsaro, an ce mafiya yawan mutanen wajen ‘yan kabilar Tajik ne, wasu mazauna yankin a Afghanistan.

Ahmad Massoud, daya daga cikin shugabannin NRF, ya shaida wa Washington Post a makon da ya gabata cewa:

“Idan mayakan kungiyar Taliban suka kaddamar da hari, ba shakka, za su fuskanci tasku daga gare mu.”

Ahmad Massoud, shi ne dan shugaban Tajikistan Ahmad Shah Massoud, wanda ake jinjinawa bisa canza kwarin Panjshir zuwa wani yanki na adawa da mayakan Rasha da Taliban.

Lardin Panjshir yana karkashin ikon NRF wanda The Khaama Press ta rawaito cewa, akalla tsoffin membobin gwamnatin biyu suna can, ciki har da ministan tsaro da mataimakin shugaban kasa na farko.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here