Gwamnatin Edo za ta Haramtawa Wadanda ba a yi wa Rigakafin Corona ba Shiga Bankuna, Ofisoshin Gwamnati da Wuraren Ibada

 

Jahar Edo – Gwamnatin Jahar Edo ta haramtawa ma’aikatan da ba su yi allurar riga-kafin corona ba shiga ofishosinsu kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Gwamnatin ta hana dukkan wadanda ba su riga sun yi riga-kafin ba shiga wuraren taruwan mutane.

Tunda farko, Gwamna Godwin Obaseki, a cikin watan Satumba, ya hana wadanda ba a yi wa rigakafi shiga bankuna, ofisoshin gwamnati da wuraren ibada.

Hakan ya janyo cece-kuce inda wata kungiya ta tafi domin hana aiwatar da dokar amma gwamnan bai sauya ra’ayinsa ba.

A ranar Talata, sakataren dindindin na ma’aikatar lafiya na jahar Edo, Osamwonyi Irowa, ya ce daga ranar 15 watan Satumban 2021 ya ce gwamnatin za ta aiwatar da dokar ‘babu katin riga-kafi, ba shiga wuraren taruwan jama’a’.

Ku saurari karin bayani …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here