Rikici ya Barke Tsakanin ‘Yan Boko Haram da ISWAP
Rikici ya barke tsakanin mayakan Boko Haram da na ISWAP a garin Sunawa.
An gano cewa ISWAP sun sace wasu mata ne masu alaka da Boko Haram
Wurin kwato matan ne mayakan Boko Haram suka halaka na ISWAP masu yawa
Gagarumar arangama tsakanin Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da mayakan ISWAP ya kawo ajalin mayakan ISWAP masu tarin yawa, HumAngle ta ruwaito.
Read Also:
Gagarumin fadan ya faru ne a yankinsa tsakanin iyakar Nijar da Najeriya. Al-Thabat, wata kafar yada labarai mai alaka da al-Qaida ta bayyana.
A wata takarda da Al-Thabat ta fitar, ta ce Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram ta halaka mayakan ISWAP a wani kauye da ake kira da Sunawa tsakanin iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.
BBC ta ruwaito cewa an fara rikicin ne bayan ISWAP ta yi garkuwa da mata masu tarin yawa wadanda ke da alaka da Boko Haram.
Babu bata lokaci kuwa Boko haram ta kai hari sansanin ISWAP din kuma ta ceto matan.
A shekarar 2016 ne bangaren Boko Haram na Shekau ya rabe daga ISWAP kuma tun daga nan suke ta samun hargitsi tare da hayaniya.