Rikici Tsakanin ‘Yan Sanda da ‘Yan Banga: Sarkin Minna, Alhaji Bahago ya Shiga Lamarin
Sarkin Minna, Alhaji Umaru Faruk Bahago, ya sanya baki a cikin rikici tsakanin kwamishinan yan sandan jihar Neja da Kwamandan kungiyar yan banga.
An dai rufe ofishoshin yan banga a fadin garin Minna bayan rundunar yan sanda ta kame tare da tsare kwamandan yan bangar, Nasiru Mohammed Manta.
Tun farko dai Manta ya zargi wasu manyan mutane a birnin da daukar nauyin bata-gari domin tayar da zaune tsaye da haifar da rashin rikici a gari.
Niger – Mai martaba sarkin Minna, Alhaji Umaru Faruk Bahago, ya shiga lamarin rikici tsakanin kwamishinan yan sandan jihar Neja, Monday Bala Kuryad da kwamandan kungiyar yan bangan jihar, Nasiru Mohammed Manta.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yan banga sun dakatar da ayyukansu bayan kama kwamandansu da tsare shi da yan sanda suka yi bisa umurnin kwamishinan yan sandan bayan kama wasu matasa da aka zarga da tayar da zaune tsaye a garin Minna.
Kwamandan yan bangan ya fadama manema labarai cewa tuni ya yi umurnin komawa bakin aiki amma baya da ra’ayin aiki tare da yan sanda.
Ya ce:
“A duk lokacin da muka yi aiki da DSS, bama samun matsala. Ina sa ran za a gudanar da bincike a tsanaki kan duk zargin da ake yi mun da yarana wanda ba shine abun da aka yi ba. An tozarta ni.
“Kuma yayin da muka koma bakin aiki a yanzu, abun da kawai za mu yi shine kallo idan kama masu laifin zai kare a tsare mu.
Read Also:
“Kun san, a duk lokacin da wadannan bata-garin suke shirin fara tsiyarsu guduwa suke yi da zaran sun hango mu. Wannan aikin tsoratar da su kadai ya isa.
Manta ya ce mutane na ta kiransa domin komawa bakin aiki, yana mai cewa zai zama laifi a gare shi idan ya nade hannu bayan kiraye kirayen da jama’a ke masa, yana mai cewa ba zai kuma raina sarkin ba.
Ya ce ya gargadi yaransa da su kasance masu bin doka sannan su janye daga aikata duk abun da ba ya cikin aikinsu a hukumance.
Jaridar Punch ta dai rahoto cewa Manta ya zargi wasu manyan mutane da daukar nauyin tashin hankali da rashin tsaro a jihar ta Neja lamarin da shine yasa shi umurnin rufe duk ofishoshin yan banga a jihar.
Manya ya bayyana cewa manyan mutanen sun yi amfani da yan sanda wajen kama shi bayan tawagarsa sun bi ta kan wasu bata-gari da ke addabar al’umma a cikin makonni uku da suka gabata.
Legit Hausa ta zanta da wasu mazauna garin Minna don ji ta bakinsu inda suka nuna jin dadinsu ga bude ofishoshin yan bangar da aka yi.
Wani mazaunin unguwar Kwangila da ke garin Minna mai suna Mallam Mansir ya ce ko shakka babu yan banga na taimakawa sosai domin yaran nan da ke haddasa fitina suna tsoronsu sosai.
Ya ce:
“Gaskiya mun ji dadin dawowar yan bijilante domin bata-garin nan suna barna sosai. Kada fa kace wasu manya ne a’a yara ne kanana yan sara suka. Akwai ranar da suka tada rikici haka suka dunga faffasa motoci da shagunan mutane a nan wajen Obasanjo complex. Da kyar aka fatattake su.
“Aikin zai fi kyau da sauki idan haka hada hannu tsakanin yan sandan da yan bijilante din domin yawanci su yan bangan sune suke zaune cikin unguwanni su suka san lungu da sako da wadannan bata garin suke.”