Rikici ya Tsinke Tsakanin ‘Yan Addini Biyu a Jahar Oyo
Bayan shekara biyu, yan addinin Oro sun sake kaiwa Musulmai hari.
Yan addinin gargjiyan sun hana kowa fita da rana saboda suna bikin shekara da suke yi.
Yan sanda sun damke mutum 3 cikin yan addinin gargajiyan.
Rikici ya barke ranar Talata a Idi-Iroko, jahar Ogun yayinda wasu yan addinin gargajiyan Oro suka kafa dokar hana kowa fita kuma suka kaiwa Malamin addinin Musulunci hari.
Jaridar Punch ta tattaro cewa yan addinin gargajiyan sun fara taron bautarsu na shekara-shekara ne tun ranar Asabar kuma suka kafa dokar hana mutane fita waje a yankin.
Read Also:
Amma abubuwa suka rincabe lokacin da suka kaiwa Musulmai hari lokacin da ake Sallar Magariba.
Hakazalika an tattaro cewa yan gargajiyan sun jikkata wani Malami, Bola Wasiu, inda ya sha sara a kai.
An ce an garzaya da shi asitibi, tare da wasu mata da yaran da aka kaiwa hari.
Wannan shine karo na biyu
Wannan shine karo na biyu da za’a kaiwa Masallata a Masallacin Umar Bin Khattab hari.
Shekaru biyu da suka gabata, an kaiwa Masallacin hari. Limamin Masallacin, Abdul Waliy Omo-Akin, ya ce yan addinin gargajiyan sun saba yarjejeniyar da aka yi da su da sauran addinai cewa su daina abubuwan bokancinsu da rana tsaka.
Yace:
“An jikkata daya daga cikin mambobinmu, Bola Wasiu, don ya fito Sallah da rana.”
“Mun samu nasarar damke mutum uku cikin maharan kuma muka mikasu hannun yan sanda.”