Manyan Attajirai 3 da Suka fi Kowa Kudi a Nahiyar Afrika

Mujallar Forbes ta fitar da sunayen manyan Attajiran Afrika a shekarar nan.

Aliko Dangote, Abdussamad Rabiu da Mike Adenuga aka samu daga Najeriya.

Abdussamad Rabiu wanda ya cika shekara 61 yau, ya ba Dala biliyan 5 baya.

Afrika – Mujallar Forbes ta fitar da jerin manyan attajiran Afrika da karin bayani game da hanyar da suka bi, suka mallaki dukiyar da suka tara a Duniya.

A shafinta na yanar gizo, Forbes ta kawo sunayen masu kudin nahiyar, wanda suka shiga cikin sahun manyan masu kudin Duniya na buga wa a jarida.

Attajiran Afrika 18 ne suka iya shiga da’irar masu kudin da ake ji da su a Duniya a shekarar 2021. Sai mutum ya na da Dala biliyan 1 sannan ake maganarsa.

Kamar yadda aka saba a shekarun bayan nan, wannan karo ma Aliko Dangote ne na farko a jerin. Har yanzu ba a samu wanda ya sha gaban shi a Afrika ba.

Ragowar masu kudin Najeriya da aka ambata a wannan jeri su ne takwaron Dangote a kasuwanci, Alhaji Abdussamad Rabiu da Mike Adenuga.

1. Aliko Dangote

Mai kudin Najeriya da Afrika, Aliko Dangote ya mallaki akalla fam Dala biliyan 12.1, idan aka yi lissafi a kudinmu na gida, ya ba sama da Naira tiriliyan biyar baya.

Hanyar samun kudi: Siminti da sukari.

Shekaru: 64 2.

Mike Adenuga

Mutum na biyu daga Najeriya a jeri shi ne Mike Adenuga wanda ya zo na biyar a fadin Afrika a wannan shekarar. Shugaban kamfanin na GLO ya mallaki Dala biliyan 6.3.

Hanyar samun kudi: Kamfanin sadarwa da harkar mai

Shekaru: 68 3.

Abdussamad Rabiu

Attajirin karshe daga Najeriya da sunansa ya fito a sahun masu kudin nahiya, wani mutumin Kano ne, Abdussamad Rabiu mai shekara 61, yana da fam Dala biliyan 5.1.

Hanyar samun kudi: Siminti da sukari.

Shekaru: 61

Ku na da labari cewa Aliko Dangote ya na gina katafaren matatar man fetur da babu irinsa a Duniya. Matatar za ta rika tace gangar danyen mai 650, 000 a kowace rana.

A taron majalisar ministoci da aka yi na makon nan, gwamnatin tarayya ta yarda za ta saye 20% na hannun jarin matatar Dangote domin a rika tafiya da gwamnati a harkar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here