Yadda Aka Samo Asalin Sunayen Jahohin Najeriya Guda 6

 

Najeriya kasa ce da ba wai kawai ta kunshi wadataccen ma’adinai da albarkatun kasa ba, ta kunshi har ma da albarkatu masu ban mamaki.

A al’adun Najeriya, babu sunan da ba shi da ma’ana kama daga sunan mutum har zuwa sunan gari.

Yayin da kowa yasan Najeriya na da jahohi 36 da babban birnin tarayya, ba kowa ne yasan ma’anar sunayen dukkan jahohin ba da kuma yadda suka samo asali.

A cikin wannan rahoton, Legit ta tattaro sunayen wasu jihohi shida da kuma yadda sunayensu suka samu a tarihi.

1. Jahar Abia

An samo sunan jahar Abia wacce aka kirkira a shekarar 1991 ta hanyar zabar harafin farko ta Aba, Bende, Isuikwuator, da Afikpo. Abia yanzu ita ce cibiyar kasuwancin jahar tare da Umuahia a matsayin babban birnin jahar.

2. Jahar Oyo

Jahar ta samo sunan ta ne daga masarautar Oyo wacce ta kasance karfin gaske kafin zuwan turawan mulkin mallaka.

Daular tana da mashahuran jarumai wadanda labarin shahararsu ta wuce masarautar.

3. Jahar Legas

Sunan Legas ya samu ne daga kalmar yaren Fotigal wanda sune Turawan farko da suka fara hulda da birnin.

Legas a yaren yana nufin tafki.

4. Jahar Ribas

Sunan jahar ya samu ne duba da yanayin tekun da ke kewaye da shi saboda yankin ya kasance mai ruwa mai yawa.

Kalmar Ribas kalma ce ta turanci da ma’anarta koguna.

5. Jahar Sokoto

Duk da cewa Sakkwato siga da aka jirkita daga kalmar Larabci “Suk” wacce take nufin kasuwa, akan kira garin da sunan Sokoto ko Sakkwato, a cewar Hausa Sakkwato birnin Shehu, tunda anan Kalifan muslunci Shehu Usmanu Dan Fodiyo ya zauna.

6. Jahar Kogi

An samo sunan jahar Kogi daga kalmar Hausa Kogi. Shahararren ruwan rudani yana cikin wannan jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here