Rikicin PDP: CNJ Tanko Muhammad ya Gayyaci Alkalai Daga Jahohi 6

 

Shugaban alkalan Najeriya, Justice Tanko Muhammad, ya gayyaci manyan alkalan jahar Rivers, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da Imo don taron gaggawa.

Wannan ya biyo bayan hukunce-hukunce masu karo da juna da ko wanne alkali cikinsu ya yanke a shari’ar siyasa.

A makon da ya gabata ne kotu biyu suka yanke hukuci mabanbanta a kan rikicin da ya kunno kai na cikin gida a jam’iyyar PDP.

FCT, Abuja – Shugaban alkalan Najeriya (CJN), Justice Tanko Muhammad ya tattaro manyan alkalan jahar River, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da Imo don taron gaggawa.

Daily Trust ta rawaito cewa, wannan ya biyo bayan hukuci mabanbanta da ko wannensu ya yanke a jaharsa masu karo da juna.

A makon da ya gabata ne kotu biyu suka yanke hukunce-hukunce masu karo da juna dangane da rikicin da ya barko jam’iyyar PDP.

Yayin da babbar kotun jahar Rivers ta dakatar da Uche Secondus daga zama shugaban jam’iyyar na kasa, sai kuma kotun jahar Kotu ta dawo da shi.

Sannan akwai hukunce-hukuncen da suka danganci wasu jam’iyoyin wadanda suka kawo rikici, Daily Trust ta rawaito hakan.

A takardar gayyatar ta ranar 30 ga watan Augustan 2021 da shugaban alkalan ya aika don gayyatar alkalan, ya na bukatar su bayyana a gaban sa don zaunawa a kan wadannan hukunce-hukuncen.

An janyo hankalina a kan illolin da hukunce-hukuncen da wasu kotu suka yanke wanda ko wanne ya ci karo da wani.

Don haka ya zama tilas a kaina in gayyace ku don mu zauna mu tattauna a kan wannan lamarin. Wannan ya ci karo da yadda NJC ya hana yanke hukunci mabanbanta musamman dangane da matsalolin cikin jam’iyya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here