‘Yan Bindiga Sun Kaiwa Coci Hari a Jahar Kogi

 

‘Yan bindiga sun kai har cocin Living Faith Church Worldwide dake unguwar Osara dake hanyar Lokoja zuwa Okene a karamar hukumar Adavi ta jahar Kogi.

Daily Trust ta rawaito cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mutum uku a cocin.

An tattaro cewa daga dirarsu cocin, yan bindigan suka fara harbin kan mai uwa da wabi domin tsoratar da mutane yayinda suke tafiya da wadanda suka sace.

Shugaban karamar hukumar Adavi, Joseph Omuya Salami, ta bakin mai magana da yawunsa, Habeeb Jamiu, ya tabbatar da cewa lallai an sace mutane uku.

Ya ziyarci wajen tare da DPOn yan sanda na Osaro domin tattauna yadda za’a ceto wadanda aka sace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here