Rikicin Siyasa: An Kashe Mutane Huɗu Ciki Har da Jami’an Tsaro a Ribas

 

An kashe aƙalla mutum biyu a jihar Ribas da ke kudu maso kudancin Najeriya lokacin da wasu matasa suka mamaye gine-gine hedikwatar ƙananan hukumomi da dama, bayan da wa’adin shugabannin ƙananan hukumomin jihar 23 ya ƙare.

Lamarin ya faru ne a jiya Talata, bayan da gwamnan jihar, Siminialayi Fubara, ya umarci shugabannin sassan mulki na ƙananan hukumomin su karɓi ragamar tafiyar da ƙananan hukumomin.

Tun a ranar Litinin aka shiga zaman ɗar-dar bayan da wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin suka lashi takobin ci gaba da zama a ofis, bisa dalilin cewa ƴan majalisar dokokin jihar 27 da ke rikici da gwamnan, waɗanda suke biyayya ga Wike sun yi wa dokar wa’adinsu kwaskwarima, ta yadda za su ci gaba da zama a muƙamansu har wata shida bayan wa’adinsu.

Duk da cewa babbar kotun jihar ta yi gyara a kan dokar, wasu daga cikin shugabannin sun lashi takobin ci gaba da zama a kan shugabancin lamarin da ya haifar da rikicin.

Da yake mayar da martani kan lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen, daya daga cikin manyan dattawan jihar, Chief Edwin Clark, ya ɗora alhakin rikicin a kan tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja a yanzu Nyesom Wike, yana mai cewa dole ne a daina siyasar ubangida a jihar ta Ribas.

Jaridar Vanguard wadda ta ruwaito labarin ta tabbatar da kisan wani ɗansanda da kuma wani ɗansakai na ƙungiyar ƴansintiri.

Haka ita ma rundunar ƴansanda ta jihar ta tabbatar da mutuwar mutum biyu sakamakon rikicin da aka gwabza tsakanin magoya bayan gwamnan da kuma tsohon ubangidan gwamnan na siyasa wato ministan na Abuja.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here