Muhammad Rili Ya Kaddamar da Muradinsa na Tsayawa Takarar Majalisa a Karamar Hukumar Ikara Dake Jahar Kaduna

Cikakken Jawabin Dan Takarar Majalisar Jihar,a karamar hukumar Ikarar jihar Kaduna, Mallam Muhammad Rili.

NASARAR MU, NASARAR IKARA CE INSHALLAH.

‘Yan uwana, Shuwagabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, yayyena, kannena,iyayena,da Kuma abokaina.

Dattawanmu masu albarka,da dukkanin masoya karamar hukumar mu ta Ikara, gaisuwa gareku cike mai cike da girmamawa.

A dukkanin rayuwata na yarda dari bisa dari da cigaban al’ummar mu ta kowane janabi,hakan tasa bana bori da sanyin jiki a duk lokacin da nasamu wata dama komai kankantarta wajen saka yankin al’ummata a farkon kowane lamari. A dukkanin rayuwata ina tsaba da tsagwaron kishin al’ummata hakance tasa nake shiga dukkan wani al’amari dazai bamu yankin mu dama nagartacciya,domin cimma kyakkyawar manufa.

Gani,gami da la’akari da cigaban da gwamnati mai adalci take yi,karkashin jagorancin shugaba abun koyi, jajirtacce, nagartacce,Kuma saitaccen gwamnan mu, Mallam Nasir El Rufa’i, yasa naji cewar ba shakka akwai rabo mai girma da yakamata al’ummar Ikara su rabauta,yiwuwar hakan zai kasance ne idan aka samu wanda zai dora tubalin ginin irin wanda mai girma Gwamna ya dora mu akan gwadaben.

Sauyin da muka gani Mai Girma Gwamna Nasir El Rufa’i ya kawo a jihar Kaduna na zama ma’auni na tabbacin cewar indai akwai shugabanci mai inganci,tsari sahihi da kwarewa da manufa,shakka babu, babu abunda bazai yiwu ba.

Muhammad rili form

A matsayina na mai biyayya domin ganin cigaban jam’iyyar mu mai albarka,kana masoyi na kwarai ga tafiya da salon mulkin mai girma gwamma,kazalika dalibin Mallam a makarantar sha’awar cigaban jihar Kaduna ta kowanne fanni musamman wajen ganin Jihar ta gilashin habbaka tattalin arziki,da zaman lafiya a Arewa Najeriya dama kasa baki daya kazalika a matsayina, na Mataimaki na Musamman ga Mai Girma Gwamna akan Cigaban Zamantakewa,ba shakka zamu kawo cigaba mai dorewa tare da hadin gwiwar nagartaccen shugabanci mai zuwa na Sanata Uba Sani,InshAllah.

Bayan dogon nazari da tsinkaye gami da tattaunawa da neman shawara daga malamai, da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, kungiyoyi,masana,shuwagabanni,maza, da mata,matasa da dukkanin rukunan al’umma, a karshe na amince da cewar zan tsaya takarar Dan Majalisar Jiha Mai wakiltar karamar hukumar IKARA.

Fatana da hangena sune da farko, Kishin Yankin mu na IKARA,fata da burin ganin yankin mu ya tsere sa’a,mun samu cigaba Mai dorewa tare da kyakkyawan hadin kai.

Fatana da mafarkina shine ganin yankin ya samar da mutane masu kyakkyawan tunani, da farin ciki yalwatacce.

A matsayina na dan jam’iyya mai biyayya ga jamiyyar mu ta All-Progressives Congress (APC) Wanda nasamu zarafin kasancewa guda daga cikin Wanda sukai takara a zabukan kananan hukumomi daya gabata,hadaka da gwargwadon ilimina,da kwarewata a shekarun ayyukana a aikin gwamnati da sauran sashikka, ba shakka ina ganin akan layin cancanta nake,domin in wakilci karamar hukumar mu ta Ikara.

Dani da mutanena munyi aiki cikin nutsuwar fitar da taswira da tsarin cigaban yankin mu domin samun dora tubalin cigaba,ba shakka zan maida hankali akan:

Ayyukan Rayya Al’umma,ta hanyar samar da kyakkyawan horon tasirin shugabanci a kowane fanni na rayuwa da habbaka harkokin kasuwanci.

Habaka tattalin arziki ta hanyar samar da tallafi.

Cigaba da ziyartar masu ruwa da tsaki domin girmamawa da dabbaka da’a da tarbiyya ga dukkanin al’ummar Ikara.

Wadannan dama wasu kyawawan manufofin sune fatanmu.

Sabili da haka na amince da tsayawa takarar Dan Majalisa a Majalisar Jihar Kaduna a kakar zabe Mai zuwa a shekarar 2023.

A ranaku da satittika masu zuwa zan cigaba da kai ziyarce ziyarce da tattaunawa daku baki daya InshAllah.

Zan rufe da yabawa gareku bisa goyon bayanku baki daya musamman ma Shuwagabannin Jam’iyya, Kansiloli na gunduma, da dukkanin jama’ar da suka halarci wannan taron.

Gaisuwa ta musamman ga kungiyoyi da daidaiku,goyon bayan ku da addu’oin ku na da matukar muhimmanci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here