RIPAN: Kungiyar Zata Saukar da Farashin Shinkafa
Kungiyar RIPAN ta yarda ta yi kasa da farashin buhun shinkafa.
‘Yan kasuwan zasu yi haka ne domin rage radadin da aka shiga.
Ana sa ran a koma saida buhu a kan N19, 000 cikin Disamban.
nan Kungiyar RIPAN ta masu aikin shinkafa a Najeriya ta amince ta rage farashin shinkafa ta yadda za a rika sayen kowane buhu a kan N19, 000.
Jaridar Daily Nigerian ta samu labari a makon nan cewa a halin yanzu ana saida kilogram 50 na buhun shinkafa tsakanin N28, 000 da N30, 000.
Rahoton da jaridar ta fitar ya bayyana cewa kungiyar RIPAN za ta karya farashin buhun shinkafa ne a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, 2020.
Read Also:
Wannan mataki yana zuwa ne bayan farashin kayan abinci sun tashi a sakamakon rufe iyakoki da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi.
Tun daga lokacin da aka hana shigo da shinkafa, wasu ‘yan kasuwa suna ta sayen buhuna rututu, suna adana wa da nufin su samu kazamar riba.
Kungiyar RIPAN ta hada kai da babban bankin kasa na CBN a farkon makon nan ta kafa wani kwamiti da zai yi kokarin ganin an samu sauki.
Shugaban kamfanin aikin shinkafa na Tiamin, Aminu Ahmed shi ne zai jagoranci wannan aiki na tabbatar da cewa an rage farashin shinkafar.
A wata hira da ya yi da jaridar, Ahmed ya tabbatar da cewa sun amince su rage farashi zuwa N19, 000 domin taimakawa gwamnati na rage radadi.
Aminu Ahmed yace masu gyaran samfarera sun karya farashinsu zuwa N160 a kan kowane kilogram, wannan zai sa ainihin buhun ya rage kudi.