Cristiano Ronaldo: Ya Warke Daga Cutar Coronavirus

Shahrarren dan wasan kasar Juventus Cristiano Ronaldo ta samu waraka daga muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus, kungiyar ta tabbatar ranar Juma’a.

“Ronaldo ya yi gwajin cutar. Sakamakon ya nuna cewa ya samu waraka,” Juventus tace. “Saboda haka, dan kwallo ya warke bayan kwanaki 19 kuma babu bukatar killace kansa yanzu.

” Ronaldo ya kamu da cutar COVID-19 ne ranar 13 ga watan Oktoba yayin wasar kasarsa, Portugal. Ya killace kansa tun lokacin da ya kowa Italiya. Shahrarren dan kwallon ya yi rashin wasanni hudu, harda wasa da tsohon abokin hamayyarsa Lionel Messi, a gasar zakarun Turai, inda kungiyarsa ta fadi ci 2-0. Kungiyar kwallon Juventus wacce ta lashe kafin Seria A a kakar da ta shude na matsayi na biyar yanzu haka a tebur.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here