Shugaban Dakarun RSF a Sudan ya yi Barazanar Kafa Gwamnatinsa
Kwamandan dakarun RSF a Sudan, ya yi barazanar kafa gwamnatinsa, inda birnin Khartoum zai kasance cibiyar gwamnatin, idan har sojojin ƙasar suka kafa mulki a birnin Port Sudan da ke gabashin ƙasar.
Cikin wani saƙon X da ya wallafa Laftanar Janar Mohammed Hamdan Dagalo,da a ka fi sani da Hemedti, ya ce RSF na nuna haƙuri kan matakai daban-daban da al-Burhan ke ɗauka don tozartar da RSF.
Read Also:
“Ba za mu yadda kowa ya yi magana a madadin ƙasar Sudan ba, tare da yin iƙirarin halastaccen shugaban,” in ji shugaban na RSF.
Barazanar shugaban na RSF na zuwa ne bayan da kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito cewa gwamnatin sojin ƙasar na shirin gina fadar shugaban ƙasa tare da shalkwatar ma’aikatar harkokin ƙasashen waje a birnin Port Sudan da ke jihar Red sea.
Birnin ya kasance wurin da gwamnati ke gudanar da ayyukanta tun bayan ɓarkewar rikici tsakaninta dakarun na RSF a birnin Khartoum cikin watan Afrilu.