El-Rufai Nuna Rashin Jin Daɗinsa Bisa Ƙaranci Masu Kaɗa Ƙuri’u a Kaduna

 

Kamar Sauran Gwamnoni , El-Rufai Ya Isa Mazaɓar Sa Domin Kada Kuri’a, Amma Ya Haɗu da Abin Ban Al’ajabi.

El-Rufai Bai tsammanin Ganin Adadin Masu Kaɗa Ƙuri’u Ya kasance Haka Fayau ba Kamar An tashi Daga Cin Kasuwa.

Sai dai Gwamnan yayi amfani da Damar Wajen nuna rashin Jin Daɗin sa Abisa Ƙaranci Masu Kaɗa Ƙuri’u a Kaduna

Kaduna – A yayin da Zaɓukan Najeriya ke cigaba da gudana kamar yadda aka tsara, majiyoyi da dama a lungu da saƙo na Najeriya na nuna yadda ake samun nasarar fitowar mutane domin kada kuri’ar da sai bayan shekaru huɗu ake kaɗawa.

An samu fitar farin ɗango a wurare da dama, a inda daga ɗaya ɓarin ba’a samu fitar jama’a ba kamar yadda aka zata.

Hakan baya rasa nasaba da fushi ko kuma halin-ko-in-kula da ƴan ƙasa ke nunawa yayin gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin wuraren da aka samu ƙamfo na mutane shine jihar Kadunan tarayyar Najeriya.

Wannan shine dalilin da daya dugunzuma hankalin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.

Malam Nasiru, yayi mamakin yadda aka samu ƙarancin masu ƙada kuri’a a cikin garin Birnin Kaduna.

Gwamnan ya bayyana haka ne sanda yake hira da masu neman labarai, jim kaɗan da hawan sa kan layi domin yin zaɓe a akwati ta 024, dake a mazaɓar Unguwan Sarki, Kaduna.

Gwamnan yace abin takaici ne ace wai wasu akwatunan babu mutane sosai, musamman yadda aka saba gani a lokutan baya kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

A cewar gwamnan: “Shugabannin da muka zaɓa yau sune zasu gudanar da lamurran jihohin ku da mazaɓun ku na shekara huɗu masu zuwa.

“Mu tuna cewa, duk sanda muka ƙiyin zaɓe, to mun bawa abokan adawar mune daman samun ƙarin ƙuria biyu ko fiye da haka,”

Inji El-Rufai

El-Rufai ya jinjinawa INEC abisa namijin ƙokari da tayi wajen haɗa wannan zaɓen, musamman ma wajen ƙirƙiro sabuwar fasaha ta tantance masu zaɓe ta (BVAS).

Inda ya ƙarƙare da cewa, da wannan fasaha, yana da tabbacin cewa za’a gudanar da zaɓe mai kyau kuma sahihi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here