Hukumar FAAN ta Shirya Rufe Filin Jirgin Saman Jahar Kebbi
Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya ta kammala shirye-shiryen rufe filin jirgin saman jahar Kebbi da ke Birnin-Kebbi, saboda gaza biyan bashin da ya kai naira miliyan 33.
Rahotanni sun nuna cewa tuni Hukumar da ke kula da sararin samaniya ta Najeriya ta umurci kamfanonin jiragen sama da su kauracewa filin jirgin mallakar gwamnatin jahar Kebbi ba tare da ba ta lokaci ba.
Read Also:
Wata majiya ta ce tuni FAAN ta kwashe ma’aikatan kwana-kwana da kuma masu ba da tsaro a filin jirgin.
Ana zargin gwamnatin jahar Kebbi da kin biyan bashin da FAAN ke binta da ya kai naira miliyan 33 tun daga watan Janairu, duk da sakonnin da hukumar ta rika tura mata na bukatar ta biya kudin.
Ko a shekarar 2019 a cewar jaridar Guardian ta Najeriya, gwamnatin jahar Kebbi ta biya FAAN bashin naira miliyan 53, bayan da hukumar ta yi barazanar kulle mata filin jirgi.
A baya FAAN ta sanar da cewa 17 daga cikin filayen jirgin sama 20 a Najeriya ba sa aiki yadda ya kamata, kuma shekaru uku ba sa samun riba duk da aiki da suke yi.