Ba Zamu Rufe Kofar Tuba ba ga ‘Yan Bindigan da Suka Mika Wuya da Sunan Tuba – Muhammad Dingyadi

 

Gwamnatin shugaba Buhari ta bayyana cewa, za ta ci gaba da yafe wa ‘yan ta’adda idan suka mika wuya.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Dingyadi ne ya bayyana haka yayin wata tattauana.

Ya kuma bayyana cewa, sojoji na ci gaba da aiki tukuru don ganin sun gama da sauran ‘yan ta’adda masu taurin kai.

Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta rufe kofar tuba ba ga ‘yan bindigan da da suka mika wuya da sunan tuba, Daily Trust ta rawaito.

Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Muhammad Dingyadi, ya bayyana hakan ne lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today, na gidan Talabijin na Channels, a daren Talata 14 ga watan Satumba.

Ministan ya ce har yanzu kofa a bude take ga ‘yan bindigan da za su mika wuya kuma su sake shiga cikin jama’a domin zaman lumana.

Ya kara da cewa ‘yan bindigan da suka tuba su ma ‘yan Najeriya ne kuma Gwamnatin Tarayya tana da alhakin sake hade su “cikin lumana da mutunci cikin al’umma”.

Ministan ya ce:

“Tabbas, su masu laifi ne, sun aikata ta’asa, sun aikata laifuka, amma bisa ga dokokin duniya, lokacin da kuka mika wuya daga fagen yaki, ba a kashe ku, ba a cutar da ku, ana ba ku damar yin magana.

“Muna sauraron su don ganin yadda za mu iya mai dasu cikin al’umma.”

Da yake magana kan hare-haren da ake kaiwa ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, musamman Katsina, Zamfara da Sakkwato, Dingyadi ya ce gwamnati za ta ci gaba da yin nasarori muddin akwai hadin kai tsakanin hukumomin tsaro.

“Za ku ga karin nasarorin da ke tafe cikin kwanaki biyu masu zuwa. Jami’an tsaro suna aiki tukuru kan sahihancin iliminsu da kwarewar kayan aikinsu don samun gagarumar nasara akan maharan.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here