‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yayan dagacin ƙauyen Sabuwar ƙasa Guda 4 a Jahar Katsina

 

Wasu miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da ‘yayan dagacin ƙauyen Sabuwar ƙasa a jahar Katsina.

Harin ya zo awanni 24 kacal bayan wasu mahara sun sace kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jahar.

A makonnin nan yan bindiga sun sace ƴaƴa, yan uwa da matan masu rike da mukaman siyasa da dama a Katsina.

Katsina – Wasu yan bindiga sun sake kai sabon hari a wani ƙauyen Katsina, inda suka sace ƴaƴan dagacin ƙauyen guda huɗu, kamar yadda Channels tv ta rawaito.

A cewar wani mazaunin ƙauyen, yan bindiga sun kai hari ƙauyen Sabuwar Ƙasa, karamar hukumar Kafur, da safiyar Litinin, inda suka yi awon gaba da ƴaƴan Alhaji Hamza Umar.

Umar, wanda shine dagacin ƙauyen Sabuwar ƙasa, yana jagorantar majalisar gudanarwa ta ƙaramar hukumar Funtua, a jahar Katsina.

Sai dai har zuwa yanzun rundunar yan sanda reshen jihar ta Katsina ba ta ce komai ba game da sace yaran dagacin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here