ƙungiya ta yi Kira ga Gwamnatin Tinubu da ya Saka Lalong a Matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya

 

Wata ƙungiya ta fara kiran Tinubu ya ba gwamnan jihar Plateau muƙamin sakataren gwamnatin tarayya a gwamnatin sa.

Ƙungiyar tace Simon Lalong ya cancanci samun wannan kujerar domin saka masa wahalar da yiwa APC.

Ƙungiyar ta kuma yi bayani kan dalilan da ya sanya take kiran Tinubu ya ba Lalong SGF a gwamnatin sa.

Jos, Plateau- Jagororin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ƙarƙashin ƙungiyar North Central APC Forum, sun yi kira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, da ya zaɓi Simon Lalong a matsayin sakataren gwamnatin tarayya a gwamnatin sa.

Rahoton Daily Trust A cewar ƙungiyar, ba Simon Lalong muƙamin na SGF zai kuma tabbatar da cewa anyi adalci a cikin gwamnati mai zuwa ta yadda kowane ɓangare zai yi na’am ya san ana damawa da shi. Rahoton Independent.

Da yake jawabi a madadin ƙungiyar a birnin Jos bayan sun gudanar da taron gaggawa, shugaban ƙungiyar Alhaji Saleh Mandung Zazzaga, yace Lalong ya wahaltawa APC, Arewacin Najeriya, a matsayin sa na shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya, jihar Plateau da zaman Tinubu shugaban ƙasa.

A kalamansa:

“Gwamna Simon Lalong yayi sadaukarwa sosai ga APC, Arewacin Najeriya, ƙasa gabaɗaya. Mutum ne mai son zaman lafiya wanda ya samu nasarori da dama kuma shugaba ne wanda baya nuna wariya. Wani abin burgewa dangane da shi shine rawar da ya taka a zaɓen shugaban ƙasa na APC.”

“Ƙungiyar mu da sauran ƙungiyoyi da wasu manyan mutane mun yi kiran da a bashi takarar shugaban ƙasa daga yankin Arewa ta Tsakiya saboda gudunmawar da yankin ya bayar, Amma ba muyi nasara ba, sai muka koma neman a bashi mataimakin shugaban ƙasa tun da an amince a miƙa mulki zuwa yankin Kudu”

“Saboda haka ƙoƙarin da Lalong yayi ya sanya yakamata a bashi matsayin SGF. Ba wai kawai ya dace da kujerar bane, amma ya cancanta kuma zai kawo ƙwarewar sa wajen shugabanci domin ciyar da ƙasar nan gaba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here