Zaben Cike Gurbi:: PDP ta Nemi da a Tsige Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa

 

Jam’iyyar PDP ta nemi hukumar zabe da ta tsige Mallam Hudu Yunusa Ari a matsayin kwamishinan zaben jihar Adamawa.

PDP na zargin Mallam Ari da nuna son kai tare da kokarin murde sakamakon zaben gwamnan Adamawa don nasarar Sanata Aisha Binani ta APC.

Babbar jam’iyyar adawar kasar ta sake gabatar da wannan bukata a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu a Abuja.

Abuja – Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta gaggauta tsige kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Mallam Hudu Yunusa Ari daga kujerarsa kafin zaben cike gurbi da za a yi a ranar 15 ga watan Afrilu.

Da yake jawabi ga taron manema labarai a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu, Debo Ologunagba, sakataren labaran PDP na kasa ya ce jam’iyyar na adawa da ci gaba da kasancewar Mallam Ari a ofis.

Ci gaba da kasancewar Ari a matsayin kwamishinan zabe zai ta da zaune tsaye, PDP

Ologunagba ya ce ci gaba da rikon kwamishinan zaben a jihar daidai yake da tunzura jama’a su yi abun da suka ga dama, rahoton Daily Trust.

Ya yi bayanin cewa bayanai abun dogaro da PDP ta samu ya nuna cewa:

“Hukumar INEC na son ta da zaune tsaye a jihar Adamawa saboda ci gaba da kasancewar Ari a matsayin kwamishinan zabe na Adamawa duk da zarginsa da ake yi da shirya munakisa don magudi a sakamakon zaben gwamna a jihar, duk da karara ya nuna PDP ce a gaba da halastattun kuri’u 31,299 a zaben.”

Zargin magudi a karamar hukumar Fufore

Kakakin na PDP ya bayyana lamarin a matsayin tsokana kuma cewa ba za su yarda INEC ta ci gaba da rikon Yunusa Ari a matsayin wanda zai kammala zaben gwamnan na ranar 15 ga watan Afrilu ba.

Ya kuma yi zargin cewa an jiyo Ari a faifan murya yana umurtan jami’in zabe a karamar hukumar Fufore cewa ya canza sakamakon zaben don nasara ya zama a bangaren yar takarar gwamnan APC, Sanata Aisha Binani, rahoton Vanguard.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here