‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Iyalan Hakimin Karamar Hukumar Tsanyawa

 

Wasu yan bindiga da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne sun farmaki gidan hakimin kauyen Nasarawa a karamar hukumar Tsanyawa, jihar Kano.

Maharan sun sace Halima Kabiru wacce mata ce ga basaraken da kuma dansa mai suna Dahiru Kabiru .

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar al’amarin inda ta ce tuni ta tura wata tawaga domin ceto mutanen ba tare da kwarzane ba.

Kano – Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutum biyu cikin iyalan hakimin kauyen Nasarawa da ke yankin karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Wadanda yan bindigar suka sace sun hada da matarsa mai suna Halima Kabiru mai shekaru 38 da kuma dansa mai suna Dahiru Kabiru dan shekaru 20 a duniya.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta yi martani

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mista Mamman Dauda wanda ya tabbatar da lamarin ya ce:

“A ranar 2 ga watan Afrilu, da misalin karfe 12:45 na dare mun samu labarin cewa wasu yan bindiga bakwai sun farmaki gidan hakimin kauyen Nasarawa sannan suka yi garkuwa da mata da dansa.

“Masu garkuwa da mutanen sun dauki wadanda abun ya ritsa da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

“Nan take muka shirya wata tawagar agaji. Yanzu haka da muke magana, tawagar na aiki ba ji ba gani don ceto mutanen da abun ya ritsa da su cikin koshin lafiya.”

CP Dauda ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici amma ya nuna karfin gwiwar cewa za a ceto mutanen sannan a kama wadanda suka sace su, rahoton The Guardian.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here