Sakataren Jam’iyyar LP na Jihar Kano ya Sauya Sheka Zuwa APC

 

Bashir Ahmad, Hadimin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari yace jam’iyya mai mulki ta ƙara karfi a mahaifarsa jihar Kano.

A cewarsa, Sakataren jam’iyyar Labour Party (LP) ya sauya sheka zuwa APC, ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu.

Wannan na zuwa ne yayin da APC ke fama da rikicin cikin gida wanda ya ja ta ɗage kaddamar da tawagar kamfe.

Kano – Yayin da ake cigaba da shirin tunkarar babban zaɓen 2023, jam’iyyar APC mai mulki ta ƙara karfi a jihar Kano, arewa maso yammacin Najeriya.

Sakataren jam’iyyar Labour Party (LP) , Nasiru Umar D. Hajiya, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, ya tabbatar da goyon bayansa ga Bola Ahmed Tinubu.

Babban mai taimaka wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na musamman kan kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad, shi ne ya bayyana haka shafinsa na Tuwita.

A rubutun da ya saki a shafinsa, Bashir Ahmad yace:

“Sakataren jam’iyyar Labour Party (LP) reshen jihar Kano ya fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulki.”

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, daga kusu maso gbaashin Najeriya, shi ke neman zama shugaban ƙasa a inuwar jam’iyyar LP, sai dai wannan cigaban ba zai masa daɗi ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here