‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Sojoji 5 a Anambra

Yan bindiga sun farmaki al’ummar yankin Umunze da ke karamar hukumar Orumba ta kudu a jihar Anambra.

Maharan da suka bude wuta sun halaka jami’an sojoji biyar da wani dan farar hula daya.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da harin amma tace bata samu cikakken bayani kansa ba tukuana.

Anambra – Jaridar The Nation ta rahoto cewa tsagerun yan bindiga sun kashe jami’an sojoji guda biyar da wani dan farin hula daya.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne a kusa da wani banki a Umunze, yankin karamar hukumar Orumba ta kudu.

Wata majiya da ta zanta da jaridar ta bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 2:00pm na ranar Laraba, 28 ga watan Satumba.

Majiyar ta bayyana cewa sojojin sun kasance a cikin wata motar Sienna ne lokacin da yan bindigar suka farmake su.

Harbe-harben ya haddasa tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.

Kakakin yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, yace an yi harbe-harbe a kusa da wani banki a Umunze.

Ya ce ba a samu cikakken bayani kan lamarin ba, yana mai cewa abun ya faru ne tsakanin 12 zuwa 12:30 na rana.

Ya kuma bayyana cewa rundunar ta tura jami’an tsaro domin kare yankin, yana mai cewa ya zama dole wadanda suka aikata ta’asar suyi danasani.

Wani babban jami’in dan sanda a jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa shima ya tabbatar da faruwar lamarin ga The Nation.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here