Masu Garkuwa Sun Saki Tsohon Shugaban NFF, Sani Ahmed Toro

Rundunar yan sandan Najeriya ta sanar da cewa masu garkuwa da mutane sun saki tsofaffin Shugabannin Hukumar Kwallon kafa ta kasar NFF.

Tun da farko masu garkuwar sun bukaci kudin fansar mutanen, da suka hada da tsohon Sakatare Janar da NFF din Sani Ahmed Toro.

Sani Toro ya shafe shekara shida yana jan ragamar NFF daga 1993 zuwa 1999.

An kuma yi garkuwa dasu ne karshen makon da ya wuce, tare da tsohon kocin yan wasan Najeriya yan kasa da shekara 23 Garba Ila da Isah Ja, a kan haryarsu ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Sai dai babu bayanai kan ko an biya kudin fansa ne kafin sakin mutanen.

Najeriya na fuskantar matsalar rashin tsaro da ya hada da garkuwa da mutane don neman kudin fansa musamman a yankin Arewa maso Yammacin kasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here