Gwamnatin Tarayya ta Shirya Samarwa da Matasa Masu Digiri Aiki

 

Gwamnatin tarayya zata saka matasa masu takardar digiri aiki na musamman na tsawon wata 12.

Rahoto ya nuna cewa shirin zai kunshi matasa yan kasa da shekara 30 aƙalla 20,000 daga faɗin ƙasa.

Ana sa ran shugaba Buhari zai sanar da lokaci da kuma yadda matasa zasu nemi shiga tsarin ranar Talata.

Abuja – Ana tsammanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai yi wata sanarwa dangane da wani shiri na musamman na matasa masu digiri ranar Talata.

FG ta kirkiri shirin ne da nufin samarwa matasa yan Najeriya da suka kammala digiri 20,000 aikin yi a wasu ɓangarorin gwamnati da kamfanoni a faɗin kasa.

Rahoto ya nuna cewa aikin matasan (yan kasa da shekara 30) zai kwashe watanni 12, kuma za’a basu cikakken albashin masu digiri.

Gwamnatin tarayya na fatan aikin zai taimaka wajen kimtsa matasan da suka kammala karatu domin gobensu da kuma muhallan aiki da zasu iya tsintar kansu nan gaba.

Menene manufar wannan shirin?

Mai taimkawa shugaban ƙasa ta ɓangaren labarai, Buhari Sallau, shine ya bayyana shirin gwamnatin a wata sanarwa da ya fitar a kafar sada zumunta Facebook.

A cewar Mista Sallau, manufofin wannan tsarin sun hada da:

“Inganta ɓangaren samar da ayyukan yi, gina matasa kan gudanar da aiki mai kyau da kwarewa a kan shugabanci, da kuma haɗa masu ɗaukar aiki da ingantattun ma’aikata.”

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa wannan shirin na gwamnatin tarayya ya samu goyon baya da tallafin daga shirin samar da cigaba na UNDP.

A ranar Talata mai zuwa ake tsammanin shugaban ƙasa Buhari zai sanar da lokacin da matasa zasu fara neman amfana da shirin a hukumance.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here