Darajar Naira ta Fadi ya yin da Dala ta Karu

 

Dalar Amurka ta kara tsada a kasuwar bayan fage a Najeriya inda ake sayar da dala daya kan naira 527 a ranar Litinin.

‘Yan kasuwa sun ce dalar ta kara tsada ne bayan da babban bankin Najeriya ya hana kananan yan kasuwa yin kasuwar ta canji a kasar.

A ranar Juma’a an sayar da dala kan naira 524 bayan rufe kasuwar. A watan da ya gabata an sayar da dala naira 525 bayan da babban bankin Najeriya ya takaita sayar da dala ga ‘yan canji, wanda ya kara sa darajar naira ta fadi a kasuwar bayan fage.

Naira Najeriya ta yi sabon faduwar da ta yi kasa da 527 akan dala a kasuwar bakar fata ranar Litinin, kwanaki bayan babban bankin ya hana kananan masu ba da bashi daga kasashen waje musayar mu’amala, ‘yan kasuwa sun ce.

Babban bankin ya hana sayar da dala ga ‘yan kasuwar canjin kan zarginsu da bin hanyoyi na halatta kudin haram.

A ranar Litinin bankunan ‘yan kasuwa suna sayar da dala kan naira 413, kusan adadin da gwamnati ta kayyade.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here