Farashin Dala ya Kara Hawa
Darajar Naira ta kai wani sabon mataki na faɗuwa inda ake canza dala ɗaya kan naira 549 a kasuwar bayan fage a ranar Litinin.
Yan kasuwa sun ce ana fama da ƙarancin dalar Amurka a kasuwa.
Read Also:
Naira ta kai matakin ne sakamakon matakan da babban bankin Najeriya ya ɗauka kan kasuwar masu canji a ƙasar.
A ranar Juma’a an sayar da dala ɗaya kan naira 545, a ranar litinin kuma ta kai naira 549.
Ana kuma sayar da dala ne kan naira 412 a farashin gwamnati a ranar Litinin.