‘Yan Bindiga Sun Kaiwa ɗaliban da ke Zana Jarabawar WAEC Hari a Jahar Imo

 

‘Yan bindiga sun afkawa ɗaliban da ke zana jarabawa ajin karshe a sakandare ta WAEC a karamar hukumar Njaba da ke Imo.

Rahotanni na cewa ‘yan bindiga sun kai hari ne adaidai lokacin da daliban ke shirin soma jarabawar, suka kora su.

Daliban da malaman sun tsere sakamakon harbe-harbe da ‘yan bindiga suka rinka yi.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa ‘yan bindiga sun cinna wuta kan baburar daliban da malaman a harabar makarantar.

Duk da cewa babu cikakun bayanai kan jikkata ko mutuwa, wani hoton bidiyo da aka rinka yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna dalibai da malamai na gudun tsira da rayukansu.

‘Yan sanda yankin ta bakin kakinta, Mike Abattam ya tabbatar da faruwar harin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here