Sanadiyyar Hatsarin Mutuwar Kanin Sarkin Daura
Abin jimami ya samu Masarautar Daura da rashin kanin sarki Alhaji Umar Faruk Umar.
Kanin Sarkin ya rasu ne a wani hatsatin mota da ta afka dashi tare da wasu mutane biyu.
Mataimakin gwamnan jihar Katsina Alh. Mannir Yakubu ya kai ta’aziyya ga masarautar.
Alhaji Abdullahi Umar Maitaro, kanin Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya rasu.Ya rasu yana da shekaru 57, Daily Trust ta ruwaito.
Maitaro da abokansa biyu sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a kauyen Muduru da ke kan hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadin da ta gabata.
Yayin da wani da ya samu raunuka ke karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Read Also:
Wadanda suka shaida lamarin sun ce motoci biyu, ciki har da na marigayin sun yi karo da juna, yayin da suke kokarin tserewa wani mai tuka a daidaita sahu wanda ba zato ba tsammani ya juyo a gabansu.
Gwamna Aminu Masari, tare da rakiyar mai ba shi shawara na musamman kan ilimi mai zurfi, Dokta Bashir Ruwangodiya, da sauran manyan jami’an gwamnati sun je Daura ranar Litinin don yi wa Sarkin ta’aziyyar rashin da aka yi.
Gwamnan ya kuma ziyarci gidajen sauran mutanen biyu da suka mutu inda ya jajantawa iyalansu.
Hakazalika, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alh Mannir Yakubu, wanda kuma shi ne Kwamishinan Aikin Gona, ya jagoranci wata tawaga a ranar Talata don yi wa sarkin ta’aziyya.
Har zuwa rasuwarsa, Maitaro ya kasance darekta a Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar Katsina.