Yadda Masana Cibiyar Nazarin Likitocin Najeriya Suka Siffanta Rigakafin Cutar Korona

 

Masana a Cibiyar Nazarin Likitocin Najeriya sun siffanta rigakafin Korona da hadari ga ‘yan Najeriya.

Masanan sun ba da bayanin cewa, ba a san yanayin dadewar rigakafin a jiki ba.

Masanan sun shawarci gwamnati ta dakata sai an samo wasu bayanai a kan rigakafin.

Masana ilimin Kawayar Cuta sun shawarci Gwamnatin Tarayya game da sayen maganin rigakafin COVID-19 a wannan lokacin, suna masu cewa ba shi da bukatar gabatar da shi yanzu ga ‘yan Najeriya.

Wata masaniyar kwayar cutar a Cibiyar Nazarin Likitocin Najeriya, Farfesa Rosemary Audu, a wata hira da ta yi da wakilin jaridar The Punch, ta ce ba za a bukaci allurar rigakafin ba idan kashi 70 cikin 100 na al’ummar kasar nan sun samar da kwayoyin kariya daga kwayar.

Ta ce, “Mun san cewa mutane da yawa sun kamu da cutar; zamu so sanin ko muna da garken kwayoyin kariya.Shin mutane suna da kwayoyin? Shin suna da rigakafin kariya tuni? Wani kashi na yawan jama’a ke da kwayoyin kariyar? .

“Idan muna da kusan kashi 70 cikin 100 na yawan jama’ar da suka samar da kwayoyin kariya game da kwayar, cutar to za mu iya cewa muna da garken kwayoyin kariya kuma ba lallai ne mu bukaci allurar ba. Wannan wani abu ne wanda na tabbata a cikin yan watanni masu zuwa ya kamata mu iya fada.

“NIMR na gudanar da bincike kan ilimin cututtuka inda muke bincika ‘yan ƙasa game da matakan kwayar kariyar su da wannan kwayar cutar. Na tabbata nan ba da jimawa ba, za mu iya bayar da shawarar ko alluran za su amfane mu ko a’a.”

Daraktan, Kimiyyar Kwayar Cutar Dan Adam da Dabbobi, na Kwalejin Kimiyya ta Jami’ar Legas, Farfesa Sunday Omilabu, a wata hira da wakilin The Punch ya ce zai zama da hadari gabatar da rigakafin COVID-19 ga ’yan Najeriya a wannan lokacin.

Ya ce, “Akwai wani abu a cikinmu wanda ke rage karfin kwayar cutar a jikinmu. Za mu iya kiranshi wani nau’in rigakafi da muke jin daɗi ta yanayinmu. Wannan yana zuwa mana a matsayin fa’ida; muna da wannan garkuwar a yanzu, idan wani abu ya shigo yanzu, zai iya lalata abin da muke amfana da shi a jikinmu.

“A gare mu, zan ba da shawarar cewa su ba mutane damar yin amfani da garken kwayoyin kariyarsu wanda suke morewa kuma kyauta ce ta dabi’a. Yakamata su maida hankali kan waɗancan mutane kadan din da ke da wasu larurar lafiya wanda ya sanya matakin garkuwar garkensu ya yi rauni sosai. Alurar rigakafin tana da haɗari yanzu saboda ba mu san yadda za ta daɗe ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here